Skip to main content

Posts

Featured

TAFIYA

I na son rubutu, Amma ni ba marubuci bane, Kayi abunda kake so karka cutu, Hakan shima ba laifi bane. Duniya da darasi, Amma mutanen ciki da koyarwa suke, Koyarwar malaman daba lasisi, Cikin duniyar yaudara muke. Aure mutuwa yake, Samarin kin aure suke, Sai yaudara ake, Dan uwa wani rayuwa kake. Yan mata na dawo dan duba, Buri, ruwan ido meye riba, Dukanin su ina cigaba, Kawar dasu, dau zaben Allah a zaba. Duniya da dadi, Wasu shafukan da daci, Mutuwa take mana ragin yadi, Alkalami tai rubutu kunji. © Alkalami Poems

Latest Posts

MASOYIYA